Shugaba Buhari Ya Kori Wasu Manyan Alkalai Biyu Daga Aiki
Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya kori wasu alkalai guda biyu na babbar kotun tarayyar kasar daga aiki, kamar yadda wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.
Rahotanni daga Nijeriya din sun ce shugaba Buharin ya sanar da korar alkalan biyu ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buharin Malam Garba Shehu ya sanya wa hannun inda ya ce shugaba Buharin ya kori mai shari'a O.O Tokode na babbar kotun tarayya dake garin Benin da kuma yi wa mai shari'a A. F. A Ademola na babbar kotun tarayya da ke Abuja ritaya ta tilas daga aiki.
Malam Garba Shehu ya ce shugaba Buharin ya dau wannan mataki na korar alkalan biyu ne bayan bayan dubi cikin shawarwarin da hukumar kula da alkalai ta Nijeriyan (NJC) ta gabatar masa a baya inda ta bukaci da a sallami alkalan biyu saboda laifuffukan da aka same su da shi. Kamar yadda kuma an umurci Mai Shari'a O.O. Tokode din da ya dawo da albashi da kuma alawus-alawus din da ya karba ba bisa ka'ida ba tun daga ranar 2 ga watan Disamban 2015 a lokacin da aka rantsar da shi a matsayin alkalin babbar kotu har zuwa yanzu.
Shi dai mai shari'a A. F. A Ademola yana daga cikin alkalan da jami'an hukumar 'yan sandan farin kaya ta Nijeriya DSS suka kama su da kuma gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin karbar rashawa da cin hanci.