Pars Today
Majiyoyin tsaro a kasar Burkina Faso sun bayyana cewar jami'an tsaro a kasar sun cafke wasu mutum shida da ake zargi da hannu a wani harin ta'addanci da aka kai birnin Ouagadougou, babban birnin kasar a watan Janairun da ya wuce.
A wani mataki na kalubalantar barazanar ta'addanci a doron kasarta, Burkina Faso na shirin janye rabin sojojinta 850 dake yankin Darfour, a cewar ma'aikatar tsaron kasar.
Kotun soja a kasar Burkina Faso ta ce zata sake neman sammacin Blaise Compaore da shugaban majalisar dokokin kasar Cote d'Ivoire Guillaume Soro, bayan wastsi da sammacin farko bisa rashin wuja mai karfi.
Kotun karya shari'a a Burkina Fasa, ta soke sammacin kasa da kasa na kotun sojin kasar kan kame tsohon shugaban kasar Blaise Compaore da kuma kakakin majalisar dokokin kasar Ivory Coast Guillaume Soro.
Shugaban kasar Burkina Faso ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin ta kawo karshen bullar duk wani aikin ta'addanci a cikin kasar.
Sabon shugaban kasa Benin Patrice Talon ya yi alkawarin yin wa'adin mulki daya, kamar yadda yayi alkawari a yakin neman zaben sa.
Mahukuntan kasar Burkina Faso sun sanar da cewa; Daruruwan 'yan kasar Ivory Coast sun tsallaka kan iyakar kasarsu domin neman mafaka a cikin kasar Burkina Faso.
Wata Kungiya dake dauke da makamai a kasar Burkina Faso ta yi barazanar kaiwa Jami'an tsaron kasar hai matukar ba a saki mutananta ba.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana tsananin damuwarsa kan yadda ayyukan ta'addanci ke kara habaka a kasashen nahiyar Afrika tare da gabatar da bukatar hada karfi tsakanin kasashen duniya domin kawo karshen ta'addanci.
Gwamnatin kasar Ivory Coast ta sanar da cewa ta ba wa hambararren shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore takardar zama dan kasar lamarin da zai iya yin kafar ungulu ga kokarin gwamnatin kasar Burkina Fason na mika mata shi don hukunta shi kan zargin da ake masa na hannu cikin kisan gillan da aka yi wa tsohon shugaban kasar Thomas Sankara