Pars Today
Amurka ta bukaci kasar China data kara matsin lambawa gwamnatin Koriya ta Arewa domin ta dakatar da shirin makamanta masu linzami da kuma na nukiliya.
Kungiyar tarayyar turai tare da China sun bayyana matsayinsu kan ci gaba da goyon bayan yarjejeniyar Paris kan dumamar yanayi, ko da kuwa Amurka ta yi watsi da yarjejeniyar.
Ministan harkokin Wajen kasar Senegal Mankor Andiyaye ya gana da mataimakin ministar harkokin wajen Sin Sin Qian Hongshan a jiya a birnin Dakar, domin bunkasa alakar kasashen biyu.
A yau ne za a yi ganawar gaba da gaba ta farko tsakanin shugabannin China da Amurka.
Wakilin kasar China a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa ta hanyar tattaunawa ce kadai za a kai ga samun nasarar warware rikicin kasar Siriya.
Kasashen Rasha da China sun hau kujerar naki dangane da wani kudurin da kasashen Turai suka gabatar a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da zargin da suke yi na cewa gwamnatin kasar Siriyan ta yi amfani da makamai masu guba a kasar.
Kasar China ta bayyana tsananin fushinta dangane da tattaunawa ta wayar tarho da zababben shugaban Amurka Donald Trump yayi kai tsaye da shugabar kasar Taiwan, da take kallon wajen a matsayin wani yanki na kasar China da ya balle.
Hukumomi a kasar China sun ce mutane 87 ne suka rasa rayukan sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da aka samu a 'yan sa'o'in da suka gabata a yankin tsakiyar gabashin kasar.
kwamitin sulhu kotun dake Hague ya yanke hukunci cewa kasar Philippines ce keda gaskia a kan tekun kudancin Sin da kasashen biyu suka jima suna takaddama a kansa.
Ministocin harkokin wajen kasashen Iran da China sun jaddada wajabcin ci gaba da kara bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu a dukkanin bangarori.