Mutane 87 Ruwan Sama Ya Kashe A China
Hukumomi a kasar China sun ce mutane 87 ne suka rasa rayukan sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da aka samu a 'yan sa'o'in da suka gabata a yankin tsakiyar gabashin kasar.
ko baya ga hasara rayuka, ruwan saman sun tilasta wa wasu miliyoyin mutane barin gidajensu, yayin da dubban gine gine kuma suka ruguje sakamakon ruwan saman a cewar rahotanni.
Bayanai sun nuna cewa akwai wata madatsar ruwa mai suna '' Three Gorges'', da ta cika makil, inda zurfin ruwan ya kai mita 164.
ruwan dai tafi yin barna sosai a lardin Hebei dake kewaye da birnin Pekin, inda zabtarewar kasa da ambaliya ta hadasa mutuwar mutane 72 da kuma batar wasu 78.
Haka zalika kuma akwai wuraren da ruwan suka hadasa barna da suka hada da lardinan Hubei, da Liaoning da kuma Henan.
A jumula mutane miliyan takwas da dari shida ne ke cikin halin kaka ni kayi a halin yanzu.