An Baiwa Philippines Gaskia Akan Tekun Kudancin Sin
(last modified Tue, 12 Jul 2016 11:18:23 GMT )
Jul 12, 2016 11:18 UTC
  • An Baiwa Philippines Gaskia Akan Tekun Kudancin Sin

kwamitin sulhu kotun dake Hague ya yanke hukunci cewa kasar Philippines ce keda gaskia a kan tekun kudancin Sin da kasashen biyu suka jima suna takaddama a kansa.

Kasar Sin dai ta jima tana ikirarin cewa yankinta ne, saidai a hukunda kotun ta yanke a dazu-sazu ta ce Sin ba tada wani hurimi akan tekun.

Kasar Philippines ce dai ta gabatar da batun gaban kotun sasantawa da ke Hague, shekaru ukun da suka wuce, tana cewa matakin da Sin ta dauka na hana ta gudanar da zirga-zirga a teku ya saba wa dokar kasa da kasa.

Tuni dai kasar ta Sin tayi wasti hukuncin kwamitin wanda tun da farko ma ta ce ba huruminsa ba ne.