Sep 29, 2018 05:55
Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran, Birgediya Janar Husain Salami, ya bayyana cewar Amurka ta gaza wajen tilasta wa duniyar musulmi bakar siyasarta yana mai cewa a halin yanzu duniya tana ci gaba da ganin yadda karfin Amurka yake ci gaba da zagwanyewa.