Pars Today
Kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ta dauki alhakin harin bindiga tare da garkuwa da mutane a wani katafaren shago da ke Kudancin Faransa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla uku.
Mai magana da yawun Sojojin Faransa Patrik Steiger ya ce; An jikkata sojojin biyar ne a wani harin da aka kai musu yankin Kidal.
Ma'aikatar shari'ar kasar Faransa ta sanar da tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy a hukumance fara gudanar da bincikensa dangane da zargin da ake masa na karbar miliyoyin Euro daga wajen tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Gaddafi don yakin neman zabensa a shekara ta 2007.
An kama Nicholas Sarkozy ne bisa zarginsa da ake yi da cin hancin da rashawa a lokacin zaben shugaban kasa na 2007.
Shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya bayyana cewa, matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka dangane da birnin Quds babban kure ne.
Ministan harkokin wajen kasar Faransa tare da tawagarsa sun iso birnin Tehran a safiyar yau Litinin don hudanar da ziyarar aikin ta kwanaki 2.
A wani lokaci nan gaba ne ake sa ran ministan harkokin wajen Faransa zai gana da manyan jami'an gwamnatin Jamhuriya Musulinci ta Iran, a ziyararsa a kasar.
Mukumomi a Faransa sun sanar dakile harin ta'addancin biyu tun daga watan Janairu da ya gabata zuwa yanzu.
Kungiyar Tarayya Turai ta yi kira da babbar murya akan a tsagaita buda wuta a yankin gabashin Ghouta na Siriya, a daidai lokacin da kwamitin tsaro ke shirin kada kuri'a kan samar da shirin tsagaita wuta a wannan yankin.
Majiyoyin tsaro a Mali, sun ce a kalla mayakan dake da'awar jihadi goma ne suka hallaka a wani harin sama da na kasa da sojin Faransa suka kai a arewacin Mali.