Mali: An Jikkata Sojojin Kasar Faransa Biyar
(last modified Thu, 22 Mar 2018 18:49:31 GMT )
Mar 22, 2018 18:49 UTC
  • Mali: An Jikkata Sojojin Kasar Faransa Biyar

Mai magana da yawun Sojojin Faransa Patrik Steiger ya ce; An jikkata sojojin biyar ne a wani harin da aka kai musu yankin Kidal.

Patrik Steiger ya kara da cewa; Bude wuta da aka yi akan rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta zaman lafiya ne ya sa sojojin suka jikkata. Kakakin sojan na Faransa ya kara da cewa tuni an kame mutane hudu da ake zargi da hannu a kai harin.

Kasar Mali ta fada cikin matsalar tsaro tun a 2012 da aka yi juyin mulki, san nan kuma da bullar kungiyoyi masu dauke da makamai a arewacin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta girke dakarunta a cikin kasar tun a 2013 domin shimfida zaman lafiya.