Kalubalen Dake Gaban Ministan Harkokin Wajen Faransa A Ziyararsa A Iran
A wani lokaci nan gaba ne ake sa ran ministan harkokin wajen Faransa zai gana da manyan jami'an gwamnatin Jamhuriya Musulinci ta Iran, a ziyararsa a kasar.
A yayin ziyarar tasa wacce ita ce irinta ta farko ta wani babban jami'in kasashen turai da suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukilkiyar Iran, Jean-Yves Le Drian zai gana da shugaban kasar ta Iran, Dakta Hassan Rohani da kuma ministan takwaransa na Iran din Mohammad Jawad Zarif a yau Litini.
Haka kuma Mista le Drian zai gana da shugaban majalisar dokokin Iran, Ali Larijani da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkhani.
Manyan manyan batutuwan da bangarorin zasu tattauna sun hada da huldar dake tsakaninsu da batun yankin gabas ta tsakiya da kuma na kasa da kasa.
Saidai Kafofin yada labarai a Faransa da dama sun yi wa ziyarar ta Le Drian da ''Ceto yarjejeniyar Nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran'' .
Faransa ta ce yarjejeniyar da aka cimma da Iran a ranar 14 ga watan Yuli na 2015 na fuskantar barazana, don haka tana bukatar tattaunawa ta kud da kud cikin natsuwa da Iran don ceto ta.
Abu na biyu kuma da Faransar ta ce zata tattaunawa kansa shi ne shirin Iran na makamai masu linzami, wanda a cewar Faransar babban abin damuwa ne gare ta da abokanta huldarta.
Sa'o'i kadan kafin zuwansa a Teheran, Jean-Yves Le Drian, a wata hira da jaridar mako- mako ta ''Dimanche'' ya yi barazana wa kasar ta Iran akan fuskantar sabbin takunkumi, idan bata natsu kan damuwar da ake da ita ba kan shirinta na makamai masu linzami.
A cewarsa ''makamman Iran masu linzami na da karfin da zasu iya cin dubban kilomita, wanda hakan ya fi karfin abunda take bukata don kare iyakokinta, wanda hakan kuma ya sabawa kudirin kwamitin tsaro na MDD'' don haka akwai barazanar Iran ta iya fuskantar sabbin takunkumi
Wannan batu na makamai masu linzami na Iran, shi ne babbar takaddamar dake tsakanin bangarorin biyu, don kuwa a cewar Iran ko da wasa baya daga cikin batun da zata tattauna a kai ba da wani.
Iran dai ta ce shirinta na makamai masu linzami na kariya ne, a don haka ba zata taba tattaunawa akan shi ba, don babu wata kasa a Turai da zata amunce a yi mata da hakan.
Shugaba Emanuel Macron na Faransa shi ne wani shugaba na kasashen Turai na farko da ya fara bukatar a gudanar da bincike mai zurfi kan shirin makamai masu linzami na Iran, bayan da shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana matsayinsa kan yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran.
A martanin da ya mayar bayan wannan furicin na Macron, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Bahram Qassemi, ya ce Jamhuriya musulinci ta Iran ba zata taba amunce shishigi na wani a cikin al'amuranta ba, face ma a cewarsa Faransa ta zamo wata aljanar gungun 'yan ta'adda munafukan Iran, wadanda ke shirya taruruka son ransu a birnin Paris, alhali suna da hannu a aikata ayyukan zubar da jini kan wadanda basu ji basu gani ba, don haka a cewar Qasemi kafin Faransa ta duba bukatocinta, to ta dubi na Iran mana.
Faransa dai ta ce batun cewa ta je Iran ne don kare manufofin Amurka ba gaskia ba ne, don kuwa ta shirya wannan ziyarar ne tun kafin jawabin Trump, saidai ta sha dage ziyarar saboda wasu dalilai.
Shugaba Trump dai ya baiwa kasashen Turai har zuwa ranar 12 ga watan Mayu mai zuwa domin su sake duba yarjejeniyar da ya danganta da ''abun asha mafi girma'' da kasashen suka aikata wanda kuma zai baida Iran damar mallakar makamman nukiliya.
Faransa dai ta ce tana so ta kare yarjejeniyar ta zamo mai karko, abun yarda ga kowa, don kalubalantarta zai iya bude gasar mallakar makaman nukiliya a yankin, sannan zai kara karfafawa Koriya ta Arewa ci gaba da shirinta na nukiliya.
Wannan kewaye kewaye da Faransa take yi, babban kalubalen dake gabansa guda daya tak ne, shi ne kashedin da Iran ta yi '' ba zamu taba tattaunawa da wani ba kan shirin makammanmu masu linzami a cewar shugaban kasar Dakta Hassan Rohani.
Daya daga cikin sharadin da Iran ta gindaya a baya bayan nan kafin shiga duk wata irin wannan tattaunawa shi ne, a cewar kakakin rundinar sojin kasar, Birgediya Janar, Seyyed Massoud Jazayeri, idan Amurka da kasashen Turai sun lalata makamman nukiliya da masu cin dogon zango da suka mallaka.