Pars Today
Yunkurin na Majalisar Dinkin Duniya, na ganin ta farfado da tattaunawar sulhu tsakanin masu rikici a Yemen, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a birnin Hodaida wanda ya kunshi tashar ruwa a yammacin kasar ta Yemen.
Kungiyar Taliban a Afganistan ta yi watsi da kiran shugaban kasar, Ashraf Ghani, na tsawaita tsagaita wuta a dalilin karshen watan Ramadan.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci a bar tashar ruwan Hudaida a bude, domin bada damar ci gaba da shigar kayan agaji a birnin, domin kaucewa kara dagula al'amuran jin kai a wannan kasa wacce aka wa kallon mafi muni a duniya.
Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana ci gaba da tattaunawa domin kaucewa zubar da jini a birnin Hodeida na kasar Yemen, inda kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kaddamar da hari a yau Laraba.
Kungiyar 'yan ta'adda ta taliban ta sanar da tsagaita buda wuta tsakaninta da sojojin Afganistan, a karshen watan Ramadan, wanda kuma shi ne irinsa na farko a cikin shekaru 17 bayan da sojojin kasashen ketare karkashin jagorancin Amurka suka kawar da mulkin daga hannun 'yan taliban din.
A Palasdinu, dubban mutane ne suka halarci jana'izar 'yar agajin nan da sojojin mamaya na Isra'ila suka kashe t aharbin bindiga a kusa da iyaka da zirin Gaza.
Rahotanni daga Jordan, na cewa akwai yiwuwar masu bore su sake fitowa, duk da kiran da Sarkin kasar, Abdallah II, ya yi ga gwamnati akan ta soke shirin nan na karin kudadden man fetur da kuma na wutar lantarki.
Shugaba Bashar al-Assad, na Siriya, ya yi barazanar yin amfani da karfi kan mayakan Kurdawa dana Larabawa dake samun goyan bayan Amurka.
Majalisar dinkin duniya ta yi kira da a kai zuciya nesa don hana kara tsananta yanayin da ake ciki a zirin gaza.
Mai bada shawara ta musamman ga shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya bayyana cewa: Kasar Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila gami da 'yar koransu Saudiyya ce suke goyon bayan ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya.