Pars Today
Babban kwamandan rundunar sojin Amurka ya ce rawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take takawa a yankin gabas ta tsakiya tana barazana ga manufofin Amurka a yankin.
Rundinar sojin Siriya ta sanar da karbe daukacin ikon birnin Damascos da gewayensa, bayan da sojojin gwamnatin kasar suka kwato tunga mafi girma da 'yan ta'adda na IS ke rike da a kudancin babban birnin kasar.
Shugaban Jamhuriya Musulinci ta Iran, Hassan Rohani, ya bayyana cewa kasarsa bata fatan barkewar wani sabon rikici a gabas ta tsakiya .
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya ce yana nazarin samar da mafita a gabas ta tsakiya tare da fira ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, sojojin gwamnatin Siriya sun kwace ikon Duma, gari na karshe dake hannun 'yan tada kayar baya a yankin gabashin Ghouta.
Rahotanni daga zirin Gaza na cewa, Palasdinawa 5 ne sukayi shahada sakamakon harbin bindiga da sojojin yahudawan mamaya na sahayoniya suka masu a ci gaba da zanga zangar da suke kan iyakar yankin da Is'ra'ila.
Kasashen duniya da suka taru a birnin Paris na kasar Faransa, sun alkawarta taimaka wa kasar Labanon da tallafin kudi da ya kai dalar Amurka sama Bilyan 11.
A karon farko tun bayan farmakin da dakarun Siriya ke kaiwa a yankin gabashin Ghouta, wani ayarin motocin 'yan tada kayar baya ya fice daga yankin.
Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane a kalla 26 ne galibi samari suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kaiwa a Kabul babban birnin kasar.
Dakarun Turkiyya da mayakan Siriya dake samun goyan bayan Ankara sun kwace daukacin ikon birnin Afrin tungar mayakan kurdawa da Turkiyyar ke kallo a matsayin 'yan ta'adda.