Duniya Ta Taimaka Wa Labanon Da Dala Bilyan 11
(last modified Fri, 06 Apr 2018 16:05:11 GMT )
Apr 06, 2018 16:05 UTC
  • Duniya Ta Taimaka Wa Labanon Da Dala Bilyan 11

Kasashen duniya da suka taru a birnin Paris na kasar Faransa, sun alkawarta taimaka wa kasar Labanon da tallafin kudi da ya kai dalar Amurka sama Bilyan 11.

Wannan alkawarin tallafin da ya kunshi kyauta da kuma rance ya fito ne a taron neman tallafi da kasar ta Labanon ta gudanar yau Juma'a a birnin Paris.

Labanon dai na neman tallafi ne don taimaka wa'yan gudun hijira Siriya dake ci gaba da kwarara a kasar

Shugaban kasar Faransa Emanuelle Macron wanda ya sanar da hakan, ya ce tallafin na sama da dala Bilyan 11 zai taimaka wa wajen samun daidaiton da muke bukata a kasar Labanon.

Bangaroron da suka bada tallafin sun hada da Faransa wacce ta sanar da taimakon dala Miliyan 550 a matsayin rance da kuma kyuta, sai kuma bankin Duniya wanda ya sanar da rancen dala Bilyan hudu, sai Saudiyya wacce ta sanar da tallafin dala bilyan guda, sai bankin Turai na BEI wanda ya sanar da Yuro Milyan 800.