Pars Today
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya fitar da wata sanarwa a yau Alhamis mai cike da nuna damuwa kan halin da al'amuran jin kai ke ciki a kasar Yemen.
Wani matashin Bafalasdine ya rasa ransa, sakamakon harbin bindiga da jami'an tsaron yahudawan mamaya na Isra'ila suka masa a yau Juma'a a yankin Hebron dake kudancin birnin Kudus.
Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane a kalla 9 ne suka rasa rayukansu a wani harin ta'addanci da aka kai a kusa da wani masallaci dake Kabul babban birnin kasar.
A wani lokaci nan gaba ne ake sa ran ministan harkokin wajen Faransa zai gana da manyan jami'an gwamnatin Jamhuriya Musulinci ta Iran, a ziyararsa a kasar.
Bayanai daga Siriya na cewa har yanzu ba'a samu damar da shigar da kayan agaji ba a yankin gabashin Ghoutta inda dubban fararen hula ke bukatar agaji gaggawa.
Kungiyar Taliban a Afganistan ta yi fatali da tayin gwamnatin kasar na bude tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu.
Sarki Salman na Saudiyya ya sallami wasu manyan jami'an sojin kasar, ciki har da babban hafsan sojin kasar, Janar Abdel Rahmane ben Saleh al-Bunyan.
Shugaba Michel Aoun, na Labanon, ya gana da takwaransa, Fuad Massum, na Iraki, a Bagadaza a wata ziyara wacce ita ce irinta ta farko da wani shugaban kasar Labanon ya taba kaiwa a wannan kasa.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya bayyana cewa farmakin da Turkiyya ke kaiwa kan mayakan Kurdawa a arewacin Siriya, ya raunana yakin da ake da kungiyar 'yan ta'adda ta IS.