Shugaban Labanon Ya Kai Ziyara Farko A Iraki
Feb 21, 2018 05:55 UTC
Shugaba Michel Aoun, na Labanon, ya gana da takwaransa, Fuad Massum, na Iraki, a Bagadaza a wata ziyara wacce ita ce irinta ta farko da wani shugaban kasar Labanon ya taba kaiwa a wannan kasa.
A yayin ziyarar, shugaba Aoun, ya bayyana anniyar kasarsa ta shiga shirin gina kasar Iraki, tare da kira ga daukacin kasashen larabawa da dai saurensu da suyi hadin gwiwa don yakar ta'addanci.
Mista Aoun, ya ce kasarsa ma ta yi fama da irin wannan matsala, amma daga bisani ta yi gagarimar nasara.
A nasa bangare, shugaban, Fuad Massum, ya ce bayan sauyin mulki, Iraki ta soma lalubo hanyoyin samun daidaito na tsakanin mazhabobi don daukar darasi daga Labanon.
Tags