MDD Ta Nuna Damuwa Kan Tabarbarewar Harkokin Jin Kai A Yemen
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya fitar da wata sanarwa a yau Alhamis mai cike da nuna damuwa kan halin da al'amuran jin kai ke ciki a kasar Yemen.
Alkalumman da MDD ta fitar sun nuna cewa mutane kimanin Miliyan 22,2 ne ke bukatar tallafi a wannan kasa ta Yemen, kwatamcin karin mutum Miliyan 3,4 idan aka kwatanta da bara.
A sanarwar da ya fitar kwamitin tsaron ya kuma nuna damuwarsa kan yadda rikicin kasar ta Yemen ke kara tsananta da kuma yadda yake shafar fararen hula.
Kwamitin tsaro ya yi kira ga duk bangarorin dake da hannu a rikicin dasu kare makarantu, asibitoci da ma'aikatansu, da kuma mutunta hurumi da 'yancin da kasar ta Yemen keda shi.
Kimanin mutane 9,300 ne suka rasa rayukansu kana wasu sama da 53,000 suka raunana a yakin da Saudiyya ta kaddamar a wannan kasa ta Yemen yau kusan shekara uku, lamarin da ya jefa kasar cikin mummunan bala'i.