Pars Today
Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriya Musulinci ta Iran ta yi fatali da zarge-zarge marar digi da mahukuntan yahudawa mamaya na Isra'ila sukayi na cewa ta yi kutse a sararin samaniyar Isra'ila.
Shuwagabannin kasashen Iran da Rasha sun jaddada cewa al'umma kasar Siriya ne suke da hakkin zabar makomarsu
Ministan harkokin wajen Qatar, Sheikh Mohamed ben Abderrahmane Al-Thani, ya fada cewa kasarsa ba zata taba kasancewa karkashin mallakar Saudiyya ba.
Shugaba Mahmud Abbas na shirin gabatar da wata bukata ga Kungiyar Tarayar Turai ta neman amincewa da Falasdinu mai cin gashin kanta.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya fada cewa wajibi ne ya tattauna tare da shugaba Bashar al-Assad na Siriya domin kawo karshen yakin basasar kasar, da kuma shirya hanyoyin da za su tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Rundinar sojin Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a yankin zirin Gaza da yahudawa suka mamaye.
Matakin shugaban Amurka Donald Trump na ayyana Qudus a hukumance babban birnin yahudawan mamaya na Isra'ila na ci gaba da shan suka daga kasashen duniya, in banda mahukuntan yahudawan da suka bayyana matakin a mastayin wani babban abun tarihi.
Kotun koli a Iraki ta sanar da soke zaben yankin Kurdistan da aka gudanar a watan Satumba da ya gabata.
Ma'aikatar harkokin waje ta Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta nuna damuwa akan yadda Faransa ke daukan bangare a rikicin gabas ta TSakiya.
A karon farko, tun bayan murabus dinsa na ba zata tun daga Saudiyya, firayi ministan Labanon, Saad Hariri, ya yi jawabi a gidan talabajin.