Faransa Na Nuna Bangarenci A Rikicin Gabas Ta Tsakiya_ Iran
Nov 17, 2017 11:12 UTC
Ma'aikatar harkokin waje ta Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta nuna damuwa akan yadda Faransa ke daukan bangare a rikicin gabas ta TSakiya.
Da yake maida martani kan kalaman da ministan harkokin wajen Faranasa Jean-Yves Le Drian ya yi a wani taron manema labarai a Riyad, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Bahram Qassemi ya ce shiga sharo ba shannu da Faransa ke yi na tare da sannin ainahin ina aka dosa ba kan iya kara rura rikicin yankin.
Qassemi ya ce damuwar da Faransa take da ita, ba ta tafiya daidai da abinda ke faruwa a yankin, sannan ya musunta duk zarge zarge marasa tushe da Faransa ta yi akan Iran nyana mai cewa sabanin hakan Saudiyya ke tada fitina a yankin.
Tags