Abass Na Neman EU Ta Amince Da Cin Gashin Kan Palasdinu
(last modified Mon, 22 Jan 2018 11:15:43 GMT )
Jan 22, 2018 11:15 UTC
  • Abass Na Neman EU Ta Amince Da Cin Gashin Kan Palasdinu

Shugaba Mahmud Abbas na shirin gabatar da wata bukata ga Kungiyar Tarayar Turai ta neman amincewa da Falasdinu mai cin gashin kanta.

Mista Abbas zai gabatar da wannan bukata ce yau a birnin Brussels a yayin ganawarsa da ministocin harkokin waje na kasashen Kungiyar ta EU.

Ministan harkokin wajen Falastdinu, Riad al-Malki ya ce, Abbas zai nemi kasashen Turai su dauki matakin ne a matsayin mayar da martini ga shugaban Amurka Donald Trump biyo bayan da ya ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin mahukuntan yahudawa sahayoniya 'yan mamaya na Isra'ila.

Kazalika Abbas zai bukaci shugabar diflomasiyar Kungiyar Tarayyar Turai, Federica Mogherini da sauran ministocin nahiyar 28 don ganin cewa sun kara kaimi a rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.