Mar 15, 2019 16:53 UTC
  • Mogherini Ta Yi Allah Wadai Kan Harin Da Aka Masallatai Biyu A New-Zeland

Babbar jami'a mai kula da harakokin siyasar wajen kungiyar tarayyar Turai ta yi Allah wadai kan harin ta'addancin da aka kai wasu masallatai biyu a kasar New-zeland.

Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya nakalto babbar jami'a mai kula da harakokin siyasar kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini na meka ta'aziyarta ga iyalan mutunan da harin ta'addanci da aka cikin wasu masallatai biyu a yankin Christchurc dake kasar New-Zeland, sannan ta ce kai hari a wuraren ibadu na a matsayin kai hari kan dukkanin dan adam.

A yayin da take bayyana alhinin  kungiyar tarayyar Turai ga kasar New-Zeland,  Moghererini ta ce kungiyar kasashen Turai a shirye take ta yi aiki tare da kasar New-Zeland a dukkanin bangarori musaman ma a fagen yaki da ta'addanci.

A nasa bangare, shugaban Majalisar Turai Antonio Tajani ya ce masu akidar babbancin launi ko kyamar baki ko kuma mahaukata ne suke kai hari a wuraren ibada.

A safiyar yau juma'a ne wasu 'yan ta'adda dauke da makamai suka kai hari cikin masallatai Lainuwud da Annor dake gefen yankin Christchurc dake kasar New-Zeland, inda suka kashe mutum 49 tare da jikkata wasu 50 na daban.

A yayin da yake Allah wadai da harin da aka kai, Firai ministan kasar New-Zeland Jacinda Ardern ya bayyana harin da ta'addanci da ba a taba ganin irinsa a kasar ba.

An bayyana cewa daya daga cikin maharan dan kasar Australiya ne.

Tags