Rasha : Putin Ya Gana Da Netanyahu A Moscow
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya ce yana nazarin samar da mafita a gabas ta tsakiya tare da fira ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Wannan bayyanin ya fito ne bayan ganawar da Mista Putin ya yi da Netanyahun a fadar Kremlin yau Laraba, wanda kume ke zuwa a washe garin ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran.
Sanarwar ta Kremlin ta ce shugaban Putin ya yi tir da kakkausar murya da matakin shugaba Donald Trump na Amurka na janye jiki daga yarjejeniyar.
Rasha da Isra'ila sun ce zasu tattauna kan batun da kuma samar da mafita.
Sanarwa ta Kremlin ta kuma ambato firaministan na Isra'ila na cewa, zasuyi nazari tare ta yadda zasu tunkari baranarar dake akwai cikin nasuwa da mutunci.
Manyan jami'an biyu kuma sun halarci wani taron tsaro, wanda a yayinsa suka tattauna kan wani hari da Isra'ilar ta kai a kusa da birnin Damscos na Siriya a cikin daren jiya.
Isra'ila dai ita ce ta farko data fara yinmaraba da matakin Trump na janje Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.