Sojojin Siriya Sun Karbe Daukacin Birnin Damascos Da Gewayensa
Rundinar sojin Siriya ta sanar da karbe daukacin ikon birnin Damascos da gewayensa, bayan da sojojin gwamnatin kasar suka kwato tunga mafi girma da 'yan ta'adda na IS ke rike da a kudancin babban birnin kasar.
Da yake bayyana hakan a gidan talabijin din kasar, kakakin rundinar sojin kasar, ya kuma ce sojojin kasar sun hallaka wani adadi mai yawa na 'yan ta'addan ''Daesh'' wanda hakan ya bada damar kwace yankin Hajar al-Aswad da kuma sansanin 'yan gudun hijira na Yarmuk.
Wannan dai na zuwa ne bayan kawo karshen kwashe mayakan dake ikirari da sunan jihadi na kungiyar ta IS da iyallansu a yankin dake kudancin birnin Damascos.
Darektan kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa OSDH, Rami Abdel Rahmane ya ce kimanin mayakan na IS da fararen hula 1,600 ne akwa kwashe daga yankin tsakanin ranakun Lahadi zuwa Litini a cikin motocin bus 32.
Dama kafin hakan sojojin na Siriya sun kwace yankunan da dama daga hannun 'yan ta'addan na IS, wadanda suka hada da yankin gabashin Ghouta da gabashin Qalamun dake arewa maso gabashin babban birnin kasar.