Yunkurin MDD, Na Farfado Da Tattauwar Sulhu A Yemen
Yunkurin na Majalisar Dinkin Duniya, na ganin ta farfado da tattaunawar sulhu tsakanin masu rikici a Yemen, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada a birnin Hodaida wanda ya kunshi tashar ruwa a yammacin kasar ta Yemen.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, na Yemen, Martin Griffiths, ya bayyana a wani taron kwamitin tsaron MDD, cewa yana sa ran sake farfado da tattaunar zaman lafiya a wannan kasa ta Yemen, a daidai lokacin da dubban jama'a ke ci gaba da kaurace wa fadan da ake a birnin na Hodaida.
Tashar ruwan Hudaida ta nan ne dai ake shigar da yawancin kayan agajin da ake taimaka wa fararen hula a kasar ta Yemen.
A wani kebaben taro tare da wakilai 15 na mambobin kwamitin tsaron, wakilin MDD, ya bayyana cewa dukkan bangarorin na Yemen suna maraba da farfado da tattaunawar ta siyasa, kamar yadda wata majiyar diflomatsiya ta shaida wa kamfanin dilnacin labaren AFP.
A watan Yuli mai zuwa ne, majalisar dinkin duniya ke sa ran kiran zagayen farko na tattaunawar, a cewar majiyar.
Yau shekaru biyu kenan da tattaunawar sulhu ta tsakanin gwamnatin Yemen mai murabus dake gudun hijira a kudancin kasar, da kuma 'yan gwagwarmayar neman sauyi da aka fi sani da 'yan Houtsis, ta cutura, wacce kuma iat ce ake ganin kawai hanyar kawo karshen rikicin da aka shiga shekaru uku anayinsa a wannan kasar ta Yemen.
Mukadashin jakadan Rasha, a MDD, Dimitri Polyanski, wanda kasarsa ke rike da shugabancin kwamitin tsaro a wannan wata, ya bayyana wa manema labarai cewa, hanyar siyasa ita ce kawai mafita ta shawo kan rikicin kasar ta Yemen, saidai ba tare da yin karin haske ba akan batun na farfado da tattaunawar zaman lafiyar na tsakanin bangarororin dake riki a kasar ta Yemen ba.
Amma wasu majiyoyuin diflomatsiyya sun bayyana cewa za'a yi tattaunawar cikin mutunta hurimi da kuma 'yancin kasar ta Yemen, ta yadda bangarorin zasu yi zaman tare cikin kwanciyar hankali.
Za'a kuma damawa da kungiyoyin farar hula da kuma kaso 30% na wakilcin mata a cikin tattaunawar da kuma gwamantin da ake fatan kafawa nan gaba.
Tattaunawar kuma zata kunshi shirin kafa gwamnatin rikon kwarya ta siyasa, da fahimtar juna kan sha'anin tsaro, da yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima, shirya zabuka da kuma hadin kan kasa.
Alkalumman da MDD, ta fitar sun nuna cewa kimanin iyalai 5,200 ne suka kaurace wa muhallansu a a birnin Hodaida, kuma har yanzu jama'a na ci gaba da kaurace wa gidajensu daga unguwanni daban-daban.
MDD dai ta ce ta damu sosai akan fadan da ake gwabzawa a birnin na Hodaida, bayan da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kaddamar da wani farmaki a makon da ya gabata a birnin Hodaida da nufin kwato shi daga hannun 'yan Houstis, lamarin da a ecwar MDD kan iya dagula al'amuran jin kai a wannan kasa ta Yemen.
A sama da shekaru uku da yakin da Saudiyya ta kaddamar a kasar ta Yemen, kimanin mutane 10,000 ne suka rasa rayukansu, a yayin da wasu milyoyi suka kaurace wa muhallansu.