Pars Today
Dubban magoya bayan sabon shugaban kasar Gambiya Adama Barrowa sun yi cincirindo a garin Bakau da ke yamma da babban birnin kasar domin nuna goyon bayansu gare shi.
Sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya ya fara gudanar da ziyarar aiki a nahiyar Afrika, inda ya fara da kasar Gambiya.
Kasar Gambia ta sanar da cewa za ta ci gaba da zama mamba a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague.
Kungiyar tarayyar Turai ta bada sanarwan bada tallafin kudade Euro miliyon 75 ga gwamnatin kasar Gambai wacce ta samu sauyin shugabanci a watan da ya gabata.
Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya sanar da dawowa kasar cikin kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukan yaki bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya janye kasar daga kotun a watannin baya.
Sojojin kungiyar kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da aka tura su kasar Gambiya don tabbatar da tsaron kasar sun sanar da cewa sun gano wasu makamai a gidan tsohon shugaban kasar, Yahaya Jammeh da can garinsa na haihuwa da ke yammacin kasar.
Babban Daraktan Bankin Duniya na yankin Afirka ya shaida cewa nan ba da jimawa ba Tawagar Bankin Duniya za ta ziyarci kasar Gambiya domin duba yadda za a taimakawa sabuwar Gwamnatin kasar.
Shugaba Adama Barrow na Gambiya ya bukaci dakarun hadaka na kasashen Afirka su ci gaba da zama a kasar tsawon watanni shida don tabbatar da lumana a kasar.
Wani na kurkusa da sabon shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya bayyana cewar a gobe Alhamis ne ake sa ran sabon shugaban zai koma kasar Gambiyan daga kasar Senegal inda ya ke zaune tun 'yan kwanaki kafin rantsar da shi da aka yi a matsayin sabon shugaban kasar.
A hukumance kasar Equatorial Guinea ta sanar da ba wa tsohon shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh masauki a kasar bayan barinsa birnin Banjul, babban birnin kasar Gambiyan a ranar Asabar din da ta gabata.