Bukatar Shugaban Gambiya na zaman Dakarun kasashen Afirka a kasar sa
Shugaba Adama Barrow na Gambiya ya bukaci dakarun hadaka na kasashen Afirka su ci gaba da zama a kasar tsawon watanni shida don tabbatar da lumana a kasar.
A cikin wani firici da yayi a wannan Alkhamis a birnin Dakar na kasar Senegal , Mohammed bn Shambas jami'in Majalisar dinkin Duniya a yammacin Afirka ya ce bukatar tsawaita zaman dakarun hadaka na kasashen Afirka a Gambiya wani lamari ne da ake ganin zai inganta tsaron kasar da ake kokonto kansa, kuma Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka Ecowas ke da alhakakin dauki mataki a kan hakan.
Masana harakokin Siyasa na ganin cewa Barazanar sojojin hadakar na kasashen yammacin Afirkan ce ta tursasawa tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ficewa daga Gambiya, inda a halin yanzu ya samu mafakar siyasa a kasar Equatorial Guinea.
Yahaya Jameh wanda ya kwashe shekaru 22 yana milki a kasar ta Gambiya ya amince da shan kayi da farko har ma ya taya sabon shugaban kasar murnar nasarar da ya samu saidai bayan wani dan Lokaci ya sauya matsayar sa dangane da sakamakon zaben inda ya yi watsi da shi, lamarin da ya harzuwa shugabanin Afirka da na Duniya har ma suka dauki matakin sauke sa da karfin tuwo.