Ziyarar Tawagar Bankin Duniya zuwa kasar Gambiya
Babban Daraktan Bankin Duniya na yankin Afirka ya shaida cewa nan ba da jimawa ba Tawagar Bankin Duniya za ta ziyarci kasar Gambiya domin duba yadda za a taimakawa sabuwar Gwamnatin kasar.
A cewar Louise Cord Babban Daraktan Bankin Duniya a yankin Afirka kwararru na bangaren harakokin Kudi na kasa da kasa za su ziyarci kasar Gambiya domin gudanar da bincike kan yanayin kudi da tattalin arzikin kasar gami da halin da Bankunan kasar ke ciki, bayan sun kammala bincikensu za su meka sakamakonsa zuwa ga bankin Duniya domin a taimaka wa kasar ta yadda za ta farfado da tattalin arzikin ta.
Kasar Gambiya dai ta fara cikin rikicin siyasa ne tun bayan da tsohon Shugaban kasar Yahaya Jammeh wanda ya kwashe shekaru 22 yana milkin kasar ya yi amai ya lashe , bayan da da farko ya amince da shan kayi a zaben shugaban da ya gabata, sannan kuma daga bisani yayi watsi da shi, saidai bayan matsin lamba da ya fuskanta daga kasashen Duniya, musaman kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka Ecowas ko Cedeao, Tsohon Shugaban Kasar ya amince da ficewa daga cikin kasar, inda yanzu haka ke samun mafukar siyasa a kasar Guine Equatorial.
A ranar Alkhamis din da ta gabata ce, Sabon Shugaban kasar ta Gambiya ya isa birnin Banjul bayan da aka rantsar da shi a ofishin jakadancin kasar dake birnin Dakar na kasar Senegal.