Pars Today
Kasa da sa'oi ashirin da hudu da kai harin kasar New Zealanda kan musulmi, an kai wani harin a kan wani musulmi a birnin London na kasar Birtaniya.
Dakarun tsaron kasar Burkina Faso sun sanar da mutuwar fararen hula 14 a yayin wani hari da wani gungun 'yan bindiga suka kai.
Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla dakarun Sojin kasar 30 ne suka mutu yayin wata fafatawarsu da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas da ke gab da kan iyakar kasar da Jamhuriyyar Nijar.
Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki kan wajen binciken ababan hawa a garin Zliten da ke gabashin birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya, inda suka kashe sojojin gwamnatin kasar hudu.
Ofishin wakilin hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya a birnin Bangi na kasar Afrika ta tsakiya ya bayyana cewa jami'an bada agaji na hukumar da sauran kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa suna fama da hare hare da kuma sata a wurare da dama a kasar.
Akalla Mutum 6 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani hari da 'yan tawayen Uganda suka kai jihar Kivo ta Arewa dake gabashin Jamhoriyar Demokaradiyar Congo.
Jami'an 'yan sandan kasar Somalia sun kaddamar da farmaki a kan babban ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke cikin birnin Magadishou fadar mulkin kasar, inda suka yi awon gaba da mataimakin ministan harkokin wajen kasar.
Kimanin mutum 18 ne suka rasa rayukansu a wani hari da mayakan boko haram suka kai yankin tabkin Tchadi.
A ranar lahadin da ta gabata ne dai wani jirgin yakin Amurka ya harba makami mai linzami akan sansanin dakarun sa-kai na Hashdush-sha'abi wanda ya yi sanadin kashe mutane 22
Majiyar sojojin kasar Libya a birnin Bangazi ta bayyana cewa wasu yan ta'adda sun kai hari kan wata ma'ajiyar man fetur a gabacin kasar sannan sun bar akalla ma'ijiya guda ta kama da wuta.