An Kashe Fararen Hula 14 A Kasar Burkina Faso
(last modified Tue, 05 Feb 2019 11:49:26 GMT )
Feb 05, 2019 11:49 UTC
  • An Kashe Fararen Hula 14 A Kasar Burkina Faso

Dakarun tsaron kasar Burkina Faso sun sanar da mutuwar fararen hula 14 a yayin wani hari da wani gungun 'yan bindiga suka kai.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Ouagadougou ya nakalto dakarun tsaron kasar Burkina Faso a jiya Litinin na cewa wasu 'yan bindiga da ake tunani 'ya'yan kungiyar nan ce mai tsatsauran ra'ayi ta kasar sun kai hari wani yanki tare da hallaka fararen hula 14.

A matsayin martani, dakarun kasar ta burkina Faso sun kai farmaki a maboyar kungiyoyi masu tsatsaran ra'ayi dake jihohi uku na arewacin kasar.

Rahoton ya ce sojojin kasar ta Burkina faso sun kai  harin ne ta kasa da ta sama tare da hallaka mutum 146 daga cikin 'ya'yan kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayi.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan rahoto.

Kimanin shekara guda kenan da kasar Burkina Fason ke fuskantar hare-hare da suka yi kama da na ta'addanci wanda ya faro daga arewacin kasar sannan kuma ya wanzu zuwa gabashi  da  iyakar kasar da kasashen Benin da Mali.

Rahoton ya ce ana danganta irin wadanda hare-haren da kungiyar ta'addancin nan mai alaka da kungiyar Alqa'ida ta yankin Magrib.