Mar 16, 2019 10:26 UTC
  • Bayan Harin New Zealand An Kai Wa Musulmi Wani Harin A London

Kasa da sa'oi ashirin da hudu da kai harin kasar New Zealanda kan musulmi, an kai wani harin a kan wani musulmi a birnin London na kasar Birtaniya.

Jaridar Indepent ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, a jiya Juma'a kasa da sa'oi 24 da kai harin da aka yi a kan masallacin musulmia  kasar New Zealand, wasu masu kyamar muslunci a birnin London na kasar Birtaniya sun kai farmaki da wukake a kan wani musulmi a  lokacin da yake fitowa daga cikin wani masallacia  birnin na Londin.

Rahoton ya ce mutane wasu ne uku daga cikin masu tsatsauran ra'ayin kin jinin musulmi a kasar ta Birtaniya suka kai harin a lokacin da aka kammala salla a cikin wani masallaci, inda suka biyu daga cikinsu suka nufi wani musulmi a lokacin da ya fito daga cikin masallacin suka yanke shi da wuka, inda suka yi masa munanan raunuka.

kafin zuwan jami'an tsaro a  wurin mutanen sun tsere, kuma babu wani wanda aka kama daga cikinsu, amma jami'an 'yan sandan London sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin.

Tags