Pars Today
Majiyar gwamnatin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta tabbatar da cewa masu dauke da makaman sun kai harin ne akan fararen hula a yankin Kivo ta arewa.
Majiyar jami'an tsaro a kasar Masar ta bayyana cewa wasu yan adawa sun kai hari kan wani ofishin yansanda a gabacin birnin Alkahira a yau Asabar.
Jami'an 'yan sandan Najeriya sun sanar da kai harin wani gungun 'yan bindiga kan mabiya kirista a kudancin kasar.
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da wani hari kan sojojin Nigeriya a Kauyen Mainok da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin kasar da nufin kwace iko da barikin soji.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kai farmaki kan wani maboyan 'yan ta'adda a lardin Sina ta Arewa, inda suka halaka wasu gungun 'yan ta'adda.
Ma'aikatar tsaron kasar Mali ta fitar da sanarwa da ta tabbatar da kai harin a tsakiyar kasar da wata kungiya mai alaka da alka'ida ta yi.
Ma'aikatar tsaron Mali ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun kaddamar da hari kan sojojin kasar a kauyen Soumpi da ke shiyar tsakiyar kasar, inda suka kashe sojojin akalla biyu.
Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ta sanar da cewa: Wasu gungun mahara sun kai harin wuce gona da iri kan jami'ar Mombasa da kudancin kasar Kenya, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu na daban.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan yankunan da suke gabar yammacin kogin Jordan, inda suka kame Palasdinawa masu yawa.
Babbban komandan dakarun Amurka a Afirka ya sanar da kai hari ta sama kan 'yan ta'adda a kasar Libiya