An Kai Hari Kan Wani Ofishin Yansanda A Kasar Masar
Majiyar jami'an tsaro a kasar Masar ta bayyana cewa wasu yan adawa sun kai hari kan wani ofishin yansanda a gabacin birnin Alkahira a yau Asabar.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto wata majiya ta yansanda a birnin Alkahira yana cewa wasu gungun yan adawa da gwamnatin kasar sun kai harin ne bayan mutuwar wani dan adawa a tsare a hannun jami'an tsaron. Gungun yan adawar sun kona motocin yansanda sannan sun doshi wasu manya manyan gine-gine na jami'an tsari a yankin ne sai yansandan suka tarwatsau da hayaki mai sa hawaye.
Majiyar ta kara da cewa mutane 9 ne suka ji rauni daga cikinsu har da jami;an yansanda biyu a lokacin fafatawan da yan adawar suka yi da yansanda a yanlin Al-Maqtam na gabacin birnin Alkahira. Jami'an tsaron dun kama mutane 20 daga cikin mutanen.
Majiyar ta kammala da cewa a jiya jumma ce wani matashin da jami'an tsaron suka kama da zargin sauda miyagun kwayoyi ya muto sanadiyyar azabtarwa a ofishin yansandan.