Jiragen Yakin Amurka Sun Kai Hari Libiya
(last modified Mon, 25 Sep 2017 05:44:28 GMT )
Sep 25, 2017 05:44 UTC
  • Jiragen Yakin Amurka Sun Kai Hari  Libiya

Babbban komandan dakarun Amurka a Afirka ya sanar da kai hari ta sama kan 'yan ta'adda a kasar Libiya

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto babban komandan dakarun Amurka a nahiyar Afirka da ake kira Africom a jiya lahadi na da'awar cewa harin baya-bayan da jiragen saman yakin kasar sa suka kai ranar juma'a a lardin Syrte dake arewacin Libiya, sun kai sa ne kan maboyan kungiyar ta'addancin nan ta ISIS.

Har ila yau babban komandan yayi da'awar cewa ya zuwa yanzu dakarun Amurka sun hallaka sama 'yan ta'addar ISIS 80 a kasar ta Libiya.

Tun bayan da Amurka tare da kungiyar tsaron Nato ta kifar da gwamnatin marigayyi kanar Mu'ammar kaddafi a shekarar 2011, kasar Libiyan ta fada cikin rikici, wanda hakan ya bawa kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya damar kutsawa cikin kasar.