Pars Today
Akalla Mutane 10 ne suka hallaka yayin da wasu da dama na daban suka ji rauni yayin wani harin ta'addanci da kungiyar Ashabab ta kai Magdushu babban birnin kasar Somaliya
Harin Bam Yayi sanadiyar Mutuwar Mutane Uku a arewacin kasar Kamaru
Sojojin Yamen da dakarun sa-kai na kasar sun kai wasu jerin hare-haren daukan fansa kan sansanonin gamayyar sojin hayar masarautar Saudiyya a garuruwan Jizan da Najran na kasar Saudiyya.
Wasu kungiyoyin fararen hula da 'yan siyasar Libiya sun bukaci daukan matakin hukunta kwamandan rundunar sojin kasar kan hadin kan da ya bai wa gwamnatin Masar wajen keta hurumin kasar ta Libiya.
A jiya alhamis ne Amurkan ta sanar da kashe fiye da fararen hula 100 a gundumar Nainawa.
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan Palasdinawa a garin Nablus da ke gabar yammacin Kogin Jordan.
Wani Jami'in tsaron wanzar da zaman lafiya na MDD dan kasar Maroko ya samu rauni sanadiyar harin da 'yan tawayen Anti-balaka suka kai sansaninsu a jamhoriyar Afirka ta tsakiya.
Mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu ya tsallake rijiya da baya a wani harin kisan gilla da wasu 'yan bindiga suka kai kan ayarinsa a yau Talata.
Majiyar tsaron Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta ce; Masu dauke da makaman magoya bayan Kamuina Nsapu ne su ka kai harin a garin na Tshimbulu.
Mutane Uku ne Su ka mutu a wani hari da masu dauke da makamai su ka kai a garin Menaka da ke arewacin Mali a yau asabar.