Mali: Harin Masu Dauke Da Makamai A Arewacin Kasar Mali.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17331-mali_harin_masu_dauke_da_makamai_a_arewacin_kasar_mali.
Mutane Uku ne Su ka mutu a wani hari da masu dauke da makamai su ka kai a garin Menaka da ke arewacin Mali a yau asabar.
(last modified 2018-08-22T11:29:38+00:00 )
Feb 04, 2017 19:26 UTC
  • Mali: Harin Masu Dauke Da Makamai A Arewacin Kasar Mali.

Mutane Uku ne Su ka mutu a wani hari da masu dauke da makamai su ka kai a garin Menaka da ke arewacin Mali a yau asabar.

 Mutane Uku ne Su ka mutu a wani hari da masu dauke da makamai su ka kai a garin Menaka da ke arewacin Mali a yau asabar.

Majiyar tsaron kasar Mali, ta ta sanar da cewa bayan harin da masu dauke da makamai a garin na Menaka, sojojin kasar sun bi sawunsu domin kama su.

Mali ta tsunduma cikin matsalar tsaro tun a 2012 bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, da kuma kutsen masu tsaurin ra'ayi a arewacin kasar.

Kawo ya zuwa yanzu sojojin kasar ba su iya samun galaba akan masu tada kayar baya ba.