Pars Today
Gwamnatin kasar Zimbabwe ta sanar da cewa akalla mutane 115 ne ake sa ran sun rasa rayukansu a wata guguwar Iska da ta taso a yankunan gabashin kasar.
Majiyar tsaro a Najeriya ta sanar da cewa; Kungiyar Boko Haram ce ta yi wa fararen hular kisan gilla a wani yanki da ke kusa da Maiduguri a jahar Borno
Kamfanin dillancin labarun Sputnik na kasar Rasha ya ambato majiyar tsaro na cewa; 'Yan Kungiyar ta Boko Haram sun kai harin ne a wani masallaci a kusa da garin Maiduguri da ke Jahar Borno a jiya asabar
Hukumomin jamhoriyar Demokaradiyar Congo sun sanar da mutuwar mutum 4 yayin gudanar da zanga-zangar dalibai a kudu maso gabashin kasar
Rahotanni daga Sudan sun ce mutanen biyu da jami'an tsaro su ka kashe su ne wani karamin yaro da kuma likita
Majiyar tsaro a kasar ta Burkina Faso ta ce an kashe sojojin uku ne a gabashin kasar ta hanyar tashin wani bom da aka girke agefen hanya
Shugaban kasar Columbia Ivan Duque Marquez ne ya sana rda kashe Walter Patrico Artizala wanda shi ne madugun 'yan tawayen kasar
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa an kashe dakarunta 8 a jamhoriyar Demokaradiyar Congo.
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: 'Yan tawayen kasar Uganda da suke da sansani a shiyar gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun kashe dakarun Majalisar Dinkin Duniya akalla bakwai.
Harin ta'addanci ta hanyar tada motoci da aka makare da bama-bamai a lardunan kasar Iraki biyu sun lashe rayukan mutane tare da jikkata wasu masu yawa.