Jan 18, 2019 12:06 UTC
  • Sudan: Mutane Biyu Sun Rasa Rayukansu A Cigaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati

Rahotanni daga Sudan sun ce mutanen biyu da jami'an tsaro su ka kashe su ne wani karamin yaro da kuma likita

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato cewa; Kungiyar likitocin kasar ta Sudan a yau Juma'a sun sanar da cewa; A jiya Alhamis ne jami'an tsaron kasar su ka kashe karamin yaro da wani likita a yayin Zanga-zangar kin jinin gwamnati a birnin Khartum

Bugu da kari sanarwar ta ce an kuma jikkata wasu mutane 10 a cikin masu Zanga-zangar

A jiya Alhamis Masu Zanga-zanga a babban birnin kasar Khartum sun nufi fadar shugaban kasa Umar Hassan al-Bashir suna masu ba da taken yin kira a gare shi da ya yi murabus

A gefe daya, shugabar kungiyar kare hakkin dan'adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta bayyana takaicinta akan yadda jami'an tsaron kasar ta Sudan suke musgunawa masu Zanga-zangar zaman lafiya

An fara Zanga-zanga ne a kasar Sudan a cikin watan Disamba na shekarar da ta gabata da ta samo asali daga hauhawar farashi kayan masarufi

Tags