Burkina Faso: An Kashe Sojoji Uku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34534-burkina_faso_an_kashe_sojoji_uku
Majiyar tsaro a kasar ta Burkina Faso ta ce an kashe sojojin uku ne a gabashin kasar ta hanyar tashin wani bom da aka girke agefen hanya
(last modified 2018-12-23T06:51:38+00:00 )
Dec 23, 2018 06:51 UTC
  • Burkina Faso: An Kashe Sojoji Uku

Majiyar tsaro a kasar ta Burkina Faso ta ce an kashe sojojin uku ne a gabashin kasar ta hanyar tashin wani bom da aka girke agefen hanya

Lamarin dai ya faru ne garin Boungou wanda yake a gabashin wannan kasar. Baya ga wadanda su ka kwanta dama, wasu sojojin hudu sun jikkata

A cikin watannin bayan nan, garin na Boungou ya fuskanci tashe-tashen hankali da kai hare-hare.

A cikin shekaru uku na bayan nan sojojin kasar ta Burkina Faso suna fada da wata kungiyar mai dauke da makamai a arewacin kasar, wacce a halin yanzu ta watsu zuwa gabashin kasar a kusa da iyakar kasashen Benin da Togo