Najeriya : Boko Haram Ta Kashe Mutane 11 A Borno
Kamfanin dillancin labarun Sputnik na kasar Rasha ya ambato majiyar tsaro na cewa; 'Yan Kungiyar ta Boko Haram sun kai harin ne a wani masallaci a kusa da garin Maiduguri da ke Jahar Borno a jiya asabar
Mutane uku ne su ka kai harin wanda baya ga kashe mutane ya kuma jikkata wasu mutanen 15
Majiyar tsaro ta ce; Maharan sun fara bude wuta ne, sannan su ka tarwartsa kawukansu a tsakanin mutanen da suke masallacin
An kai harin ne a adaidai lokacin da kasar ta najeriya take fuskantar manyan zabuka da su ka kunshi na shugaban kasa da na 'yan Majilisun dokoki da dattijai
Kungiyar boko haram ta fara kai hare-hare ne a Najeriya tun a 2009 wanda yawo ya zuwa yanzu fiye da mutane 20,000 sun kwanta dama. Bugu da kari rikicin ya tilastawa wasu mutane fiye da miliyan biyu yin hijira daga gidajensu zuwa in da za su sami mafaka
Bugu da kari kungiyar ta boko haram tana a matsayin barazanar tsaro ga kasashen da suke makwabtaka da Najeriya da su ka hada, Nijar, Kamaru, da Chadi