Yan Tawayen Uganda Sun Kashe Dakarun MDD A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: 'Yan tawayen kasar Uganda da suke da sansani a shiyar gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun kashe dakarun Majalisar Dinkin Duniya akalla bakwai.
A sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a jiya Alhamis ta bayyana cewa: A wani dauki ba dadi da aka yi tsakanin dakarunta da suke aikin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da 'yan tawayen kasar Uganda na kungiyar Allied Democratic Forces a garin Beni da ke lardin Kivu ta Arewa a shiyar gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, dakarun Majalisar Dinkin Duniya bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da guda ya bace babu labarinsa kuma wasu goma da na daban suka samu raunuka.
Har ila yau gumurzun ya lashe rayukan sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo masu yawa tare da jikkata wasu adadi na daban da suke tallafawa dakarun Majalisar Dinkin Duniya a yankin na garin Beni da ke gabashin kasar.
Tuni kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da tofin Allah tsine kan wannan ta'asa ta kungiyar 'yan tawayen Uganda ta Allied Democratic Forces.