Pars Today
Jamia'an tsaron Jamus sun sanar da cewa suna ci gaba da gudanar da bincike a kan wasu Turkawa 20 bisa zarginsu da yi wa gwamnatin Turkiya leken asiri a cikin kasar ta jamus.
A yayin dake kakkausar Suka kan firicin Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan da ya yi a kan Shugaban Gwamnatin Jamus, Ministan Harakokin wajen kasar ya ja kunan Shugaban kasar na Turkiya
Bayan barazanar kaddamar da harin ta'addanci a wata cibiyar kasuwanci da ke birnin Essen na kasar Jamus, jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kame wasu mutune biyu kan zargin hannu a shirya kai harin.
Jami'an diflomasiyyar kasar Trkiya 136 ne suka nemi mafakar siyasa daga gwamnatin kasar Jamus, wadanda dukkaninsu suna dauke ne da fasfo na diflomasiyya.
Gwamnatin Jamus ta sanar da cewa: 'Yan kasar Turkiyya da yawansu ya kai 136 kuma mafi yawansu masu dauke da takardar izinin tafiye-tafiye na jakadanci ne suke neman mafaka a cikin kasarta.
Gwamnatin kasar Jamus ta bada sanarwan haramta sayar da wasu kayakin wasan yara mai suna Genesis Toys kirar wani kamfanin AMurka
Ministan Tsaron Kasar Tanzaniya Husain Mwini ya ce; Kasarsa tana da niyyar neman, Jamus ta biya ta fansa akan mummunan mulkin mallakar da ta yi mata.
Jami'an gwamnatin kasar Jamus na ci gaba da nuna rashin amincewarsu da irin salon siyasar shgaban kasar Amurka Donald Trump.
Majiyar labarai daga kasar Jamus ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun kama mutane ukku wadanda suke aiki da kungiyar yan ta'adda ta Daesh daga kasar Iraqi da siria.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta mayarwa da zababen shugaban kasar Amurka Donald Trump martani dangane da kalamen da yayi na cacakar tarraya Turai.