Merkel, Ta Mayarwa Da Trump Martani
(last modified Mon, 16 Jan 2017 17:44:49 GMT )
Jan 16, 2017 17:44 UTC
  • Trump, ya ce Merkel ta yi kuskure data karbi \'yan gudun hijira a kasarta
    Trump, ya ce Merkel ta yi kuskure data karbi \'yan gudun hijira a kasarta

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta mayarwa da zababen shugaban kasar Amurka Donald Trump martani dangane da kalamen da yayi na cacakar tarraya Turai.

Da take amsa tambayoyin manema labari dangane da kalamen na Mr Trump, waziyar ta Jamus Angela Merkel ta ce makomar kasashen turan na ga hannunsu.

Ta kara da cewa ina ga kasashen Turai sun san makomarsu, kuma zata kara yin iyakacin kokarin ta na ganin kasashe 27 mambobin kungiyar sunyi aiki tare akan makomarsu.

Shi dai Mr Trump ya yaba da matakin kasar Biritaniya na ficewa daga kungiyar Turai, wanda ya ce abu ne mai kyawo kuma wanda ya kamata sauren kasashe suyi koyi da hakan.

Hakazalika zababen shugaban kasar ta Amurka da zai yi rantsuwar kama aiki a ranar Juma'a mai zuwa ya soki matakin kasashen Turan na karbar 'yan gudun hijira musamen Mme Angela Merkel wanda ya ce duk da yana mutunta ta, aman tayi babban kuskure akan karbar 'yan gudun hijira zuwa kasar.