An Kama Wasu Mutane Ukku Wadanda Suke Aiki Da Kungiyar Daesh
(last modified Wed, 01 Feb 2017 06:23:43 GMT )
Feb 01, 2017 06:23 UTC
  • An Kama Wasu Mutane Ukku Wadanda Suke Aiki Da Kungiyar Daesh

Majiyar labarai daga kasar Jamus ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun kama mutane ukku wadanda suke aiki da kungiyar yan ta'adda ta Daesh daga kasar Iraqi da siria.

Wata jaridar kasar Jamus mai suna Bild ya bayyana cewa mutanen ukku suna kai kawo zuwa wasu cibiyoyi na yan ta'adda a birnin na Balin tun bayan hare haren ta'addanci da aka kai da mota a cikin birnin  Balin babban birnin kasar a cikin watan Decemba da ya gabata.

Majiyar labaran ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun dade suna bin sawon wadannan mutane ukku har tun bayan harin  har kuma suka gano cikekken aikinsu a cikin kungiyar ta Deash. 

Da dama daga cikin mayakan kungiyar ta Daesh yan kasashen turai ne suka koma gida bayan an koresu daga kasashen syria da iraqi, sannan suke kokarin kai hare haren ta'addanci a kasashen nasu.