Pars Today
Shugaban Gwamnatin Jamus ta daukin kayin da Jam'iyyarta ta sha a birnin Berlin
Daruruwan mutanen kasar Jamus sun gudanar da wata zanga-zangar kin jinin mahukutan Saudiyya a birnin Berlin na kasar Jamus suna masu Allah wadai da abin da suka kira "danyen aikin" da mahukuntan Saudiyyan suke aikatawa a duk fadin duniya.
Ministan harakokin wajen Jamus ya bukaci dukkanin bangarorin dake fada da juna a kasar Siriya da su zartar da yarjejjeniyar da aka cimma tsakanin kasashen Rasha da Siriya
Ministan cikin gida na Jamus ya nemi da a haramta saka hijabi a kasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara akan hanyoyin inganta tsaro da yaki da tsatsaran ra'ayin addini a kasar.
Kungiyar kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekaru 23 ta Nigeria ta gaza kai wa ga wasan karshe na kwallon kafa na maza a wasan Olympics da ake yi a kasar Brazil bayan da ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Jamus a daren jiya Laraba.
Kasar Jamus ta sanar da wani shiri na tsaurara matakan tsaro da nuna halin ba sani ba sabo kan wadanda ake zargi da ayyukan tashin hankali da nufin fada da ayyukan ta'addanci da suke barazana ga kasar.
Mataimakin Shugabar Gwmanatin Jamus, Ba Turkiya Babu Shiga Turai Har Shekaru 20
Fadar shugaban kasa a Turkiyya ta yi allawadai da matakin da kotun tsarin mulkin Jamus ta dauka na hana watsa wani jawabin shugaban kasar Racep tayib Erdogan kai tsaye ga al'ummar kasarsa dake ganganmi a birnin Cologne na kasar Jamus a yau.
A Jamus mutane 12 ne suka raunana bayan da wani matashi ya tayar bom a wani gidan cin abinci dake tsakiyar birnin Ansbach a kudancin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi tofin Allah tsine kan harbe-harben da aka yi a cibiyar kasuwanci da ke birnin Munich na kasar Jamus a jiya Juma'a.