Kasar Jamus Ta Doke Nijeriya A Gasar Kwallon Kafa Na Olympic
(last modified Thu, 18 Aug 2016 05:35:02 GMT )
Aug 18, 2016 05:35 UTC
  • Kasar Jamus Ta Doke Nijeriya A Gasar Kwallon Kafa Na Olympic

Kungiyar kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekaru 23 ta Nigeria ta gaza kai wa ga wasan karshe na kwallon kafa na maza a wasan Olympics da ake yi a kasar Brazil bayan da ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Jamus a daren jiya Laraba.

Kasar Jamus din ta fara zura kwallonta na farko kimanin mintoci 9 da fara wasan ta hannun dan wasanta Lukas Klostermann duk kuwa da kokarin da 'yan wasan Nijeriyan suka yi na fanshewa amma abin ya ci tura har aka je ga hutun rabin lokaci, Jamus tana da kwallo guda a ragar Nijeriya.

Bayan dawowa hutun rabin lokacin kungiyoyin biyu sun ta kai bara wa junansu, 'yan Nijeriyan suna kokarin fanshewa su kuma 'yan Jamus suna kokarin karawa ko kuma kiyaye kwallo guda din da suka sa har kusan karshen watan inda ta samu nasarar sanya kwallo na biyu a ragar Nijeriyan ta hannun dan wasanta mai suna Nils Petersen.

Da wannan sakamakon dai kasar Jamus din ta kai wasan karshe na gasar inda za ta kara da kungiyar kwallon kafa na Brazil wacce ita ma a jiyan ta lallasa kasar Honduras da ci 6-0.

Kungiyar kwallon kafa ta Nigeria da aka fi sani da "Dream Team" za ta kara da kasar Honduras don neman wanda zai zama sami matsayi na uku a gasar da kuma samun kambin tagulla na gasar.