-
'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Sun Sako Wasu Matuka Jirgin Kasar Kenya Bayan Biyan Kudin Fansa
Feb 20, 2018 05:17'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun sako wasu matuka jirgin saman kasar Kenya guda biyu da suke rike da su bayan sun karbi kudin fansa da diyyar wani mutum da aka kashe a lokacin da jirgin matukan biyu yayi hatsari a watan da ya gabata.
-
An Hallaka 'Yan Sandar Kenya Biyu A Kan Iyaka Da Somaliya
Feb 15, 2018 11:13Kwamishinan 'yan sanda na yankin arewa maso gabashin kasar kenya ya sanar da mutuwar jami'ansa biyu a wani gumurzu da aka yi a kan iyakar kasar da kasar Somaliya
-
Kenya : An Bude Gidajen Talabijin 2 A Aka Dakatar
Feb 05, 2018 16:23A kasar Kenya, biyu daga cikin goddajen talabijin uku da gwamnatin kasar ta dakatar watsa shirye shiryensu a ranar 30 ga watan da ya gabata sun fara aiki a yau Litini.
-
Jami'an Tsaron Kenya Sun Kame Daya Daga Cikin Manyan 'Yan Adawar Kasar
Feb 02, 2018 12:18Jami'an tsaron Kenya sun kai farmaki gidan daya daga cikin manyan 'yan adawar kasar da ke birnin Nairobi fadar mulkin kasar tare da kame shi a safiyar yau Juma'a.
-
Kenya Ta Yi Watsi Da Umurnin Kotu Na Kawo Karshen Dakatar Da Tashoshin Talabijin 3 A Kasar
Feb 02, 2018 06:23Gwamnatin kasar Kenya ta yi watsi da umurnin wata babban kotu a kasar wacce ta bukaci ta kawo karshen dakatar da watsa shirye-shirye na wasu tashoshin talabijan guda uku masu zaman kansu, wadanda ta bada umurnin dakatar da watsa shirye-shiryensu bayan da suka soma watsa bukin rantsar da madugun yan adawar kasar Raila Odinga a ranar Talatan da ta gabata.
-
Kenya : Ana Zaman Dar-dar Gabanin Ranstuwar Odinga
Jan 30, 2018 06:24A Kenya ana cikin zaman dar-dar a daidai lokacin da jagoran 'yan adawa na kasar Raila Odinga, ke shirin rantsar da kansa a matsayin shugaban kasar.
-
An Kama Mata 10 Yan Kasashen Waje Kan Zargin Safarar Mutane A Kasar Kenya
Jan 08, 2018 06:39Majiyar Jami'an tsaro a kasar Kenya ta bada labarin cewa sun maka mata 10 yan kasashen waje a tashar jiragen ruwa ta Mombasa kan zargin safarar mutane zuwa kasashen waje.
-
Kenya : An Aikata Muggan Laifuka A Lokutan Zabe_ HRW
Dec 15, 2017 05:47Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa, Human Rights Watch, ta fitar da wani rahoto dake cewa an ci zarafi da kuma aikata miyagun laifuka a lokutan zaben da ya gabata a kasar Kenya.
-
'Yan Adawa A Kenya Sun Sanar Da Shirin Rantsar Da Raila Odinga A Matsayin 'Shugaban Al'umma'
Dec 09, 2017 16:59Gamayyar jam'iyyun adawa na kasar NASA sun sanar da wasu tsare-tsare da suke da shi na rantsar da magudun 'yan adawan kasar Raila Odinga a matsayin abin da suka kira 'shugaban kasa na al'umma' lamarin da ake ganin zai iya sake sanya kasar cikin wani rikici na siyasa.
-
An Rantsar Da Shugaba Uhuru Kenyatta A Wa'adin Shugabancinsa Na Biyu
Nov 28, 2017 19:05Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi rantsuwar kama aiki a wa'adin shugabancinsa na biyu kuma na karshe a babban filin wasanni na birnin Nairobi fadar mulkin kasar a yau Talata.