-
A Yau Ne Za A Rantsar Da Shugaba Kenyatta A Matsayin Shugaban Kenya Karo Na Biyu
Nov 28, 2017 05:19A wani lokaci a yau din nan Talata ce ake sa ran za a gudanar da bukukuwan rantsar da shugaba Uhuru Kenyatta a wa'adi na biyu kuma na karshe na shugabancin kasar Kenya a daidai lokacin da 'yan adawa suka sha alwashin gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da hakan.
-
Kenya : Kotun Koli Ta Yi Na'am Da Sake Zaben Kenyatta
Nov 20, 2017 10:03Kotun koli a kasar Kenya ta amince da sake zaben shugaba Uhuru Kenyatta a wani wa'adin shugabanci na shekaru biyar masu zuwa.
-
Kenya: An Kashe 'Yan Hamayyar Siyasa 5 A Yau Juma'a
Nov 17, 2017 18:56"Yan sandan kasar ta Kenya sun ce 'yan daba ne suka kashe magoya bayan jagoran adawa Reila Odinga.
-
An Shiga da Kararaki Biyu Bayan Zaben Kenya
Nov 07, 2017 16:28Wasu bangarori biyu a kasar Kenya sun gabatar da kakaraki gaban kotun kolin kasar inda suke kalubalantar zaben shugaban kasa da Shugaba Uhuru Kenyata ya sake lashewa da kashi 98% na ywan kuri'un da aka kada.
-
Kungiyar AU Ta Jinjinawa Zaben Kenya
Nov 01, 2017 05:44Masu sa ido na kungiyar hadin kan Afirka AU a zaben kasar Kenya da aka sake, sun yi na'am da sakamakon zaben, suna masu kira ga masu ruwa da tsaki a siyasar kasar da su tattauna da juna, ko a kai ga kawo karshen rarrabuwar kai tsakanin al'ummar kasar.
-
Gwamnatin Kenya Ta Kare Batun Rashin Fitowar Mutane A Zaben Shugaban Kasar
Oct 28, 2017 18:02Gwamnatin kasar Kenya ta bayyana cewar shugaban kasar Uhuru Kenyatta zai zama halaltaccen shugaban kasa matukar aka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 26 ga watan Oktoba din nan duk kuwa da karancin fitowar mutane a zaben.
-
Dauki Ba Dadi Tsakanin 'Yan Sandan Kenya Da 'Yan Adawar Kasar Ya Lashe Ran Mutum Guda
Oct 28, 2017 11:50A wani sabon rikici tsakanin rundunar 'yan sandan Kenya da gungun 'yan adawar siyasar kasar ya lashe ran mutum guda tare da jikkatan wasu adadi na daban a garin Bungoma da ke yammacin kasar ta Kenya.
-
Gumurzu Tsakanin 'Yan Sandan Kenya Da 'Yan Adawar Kasar Ya Lashe Rayukan Mutane Uku
Oct 26, 2017 18:50Dauki ba dadi tsakanin 'yan sandan Kenya da 'yan adawar kasar da suka kauracewa zaben shugabancin kasar da ake sake gudanarwa a yau Alhamis ya lashe rayukan mutane akalla uku tare da jikkatan wasu adadi na daban.
-
An Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar Kenya Yayin Da Ake Sake Zaben Shugaban Kasar
Oct 26, 2017 05:49Rahotanni daga kasar Kenya sun bayyana cewar an dau tsauraran matakan tsaro a duk fadin kasar a daidai lokacin da aka shirin sake gudanar da zaben shugaban kasar a karo na biyu a yau din nan Alhamis duk kuwa da kaurace wa zaben da madugun 'yan adawan kasar Raila Odinga yayi.
-
Gamayyar 'Yan Adawar Kenya Ta National Super Alliance Ta Haramta Zaben Shugabancin Kasar
Oct 24, 2017 06:40Wata gamayyar jam'iyyun adawar Kenya ta National Super Alliance ta sanar da cewa: 'Yan adawar Kenya sun zartar da hukuncin haramta zaben shugabancin kasar da za a sake gudanarwa a ranar 26 ga wannan wata na Oktoba.