Kungiyar AU Ta Jinjinawa Zaben Kenya
Masu sa ido na kungiyar hadin kan Afirka AU a zaben kasar Kenya da aka sake, sun yi na'am da sakamakon zaben, suna masu kira ga masu ruwa da tsaki a siyasar kasar da su tattauna da juna, ko a kai ga kawo karshen rarrabuwar kai tsakanin al'ummar kasar.
Masu sa idon dai sun bayyana zaben wanda bai samu yawan masu kada kuri'u ba, a matsayin wanda ya dace da tanaje tanajen kundin tsarin mulkin kasar Kenya.
Rahotanni sun bayyana cewa, rashin kyawun yanayi, da kuma tarzoma a wasu yankuna da ke da yawan 'yan adawa a kasar sun gurgunta zaben a wasu sassa.
Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu ne Thabo Mbeki ya jagoranci tawagar AU don gani yadda zaben ya wakana, duk da cewa 'yan adawa sun kauracewa shiga a dama da su a zaben karo na biyu.
A ranar Litinin ne hukumar zaben Kenya ta ayyana shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya sake lashe zaben na ranar 26 ga watan oktoba da ya shige, da kimanin kaso 98.26% na jimillar kuri'un da aka kada.