An Shiga da Kararaki Biyu Bayan Zaben Kenya
Wasu bangarori biyu a kasar Kenya sun gabatar da kakaraki gaban kotun kolin kasar inda suke kalubalantar zaben shugaban kasa da Shugaba Uhuru Kenyata ya sake lashewa da kashi 98% na ywan kuri'un da aka kada.
Bangarorin da suka da wani tsohon dan majalisa da wasu kungiyoyi biyu sun kalubalanci zaben, inda tsohon dan majalisar mai suna John Harun Mwau ke cewa an sabawa tsaida dan takara da ya fafata da shugaba Uhuru a zagaye na biyu, inda ya bukaci kotun data sake soke zaben kamar na ranar 26 ga watan jiya kamar yadda ta yi a waccen zaben na ranar 8 ga watan Agusta.
Ya ce kamata ya yi kotunta sake tantance wani dan takara da zai fafata da shugaba Uhuru.
bnaya ga shi dai wasu jagororin kungiyoyi da sukia hada kwamitin kasa da kasa na alkalan reshen kasar ta Kenya da darektan kungiyar yancin musulmi ta Muhuri shi ma ya shiga da kara inda suka kalubalanci zaben da cewa ba'a bi hanyoyin kiran zaben ba, bisa la'akari da korafe-korafen jagoran 'yan adawa na kasar Raila ODinga.
Kotun kolin kasar dai na da kwanaki 14 domin duba korafe korafen bangarorin.