Gwamnatin Kenya Ta Kare Batun Rashin Fitowar Mutane A Zaben Shugaban Kasar
Gwamnatin kasar Kenya ta bayyana cewar shugaban kasar Uhuru Kenyatta zai zama halaltaccen shugaban kasa matukar aka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 26 ga watan Oktoba din nan duk kuwa da karancin fitowar mutane a zaben.
Sakatarenn sadarwa kan kuma kakakin fadar shugaban kasar Kenyan Manoah Esipisu ne ya sanar da hakan a wata tattaunawa da yayi da tashar talabijin din CNN ta kasar Amurka inda ya ce sakamakon farko-farko na zaben na nuni da cewa shugaba Kenyattan yana kusa samun kuri'un da ya samu a zaben da aka gudanar wanda kotun kolin kasar ta soke, don haka babu abin da zai hana shi zama halaltaccen shugaban kasa.
Mr. Manoah Esipisu ya kara da cewa a dabi'an sake gudanar da zabubbuka a karo na biyu na fuskantar matsalar rashin fitowar al'umma, kamar yadda ake iya ganin hakan a cikin zabubbukan da aka gudanar a kasashen Romaniya da Kosovo da ma Ethiopia a shekarar nan, duk kuwa da cewa su din ma babu rikici da kiran da a kaurace.
'Yan adawan kasar Kenyan dai suna sa alamun tambaya dangane da halalcin zaben ne sakamakon rashin fitowar al'umma wanda aka ce mutanen da suka fito ba su wuce kashi 34.5% ba .
A nan gaba ne dai ake sa ran za a sanar da sakamakon zaben wanda alamu na nuna cewa shugaba Kenyattan shi ne zai lashe shi.