-
Raila Odinga Dan Takarar Gamayyar Jam'iyyun Adawa A Kenya Ya Janye Daga Takara
Oct 11, 2017 06:30Shugaban gamayyar jam'iyyun adawa a zaben shugaban kasa wanda za'a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa a kasar Kenya ya bayyana janyewarsa daga takarar.
-
Wasu Mahara Sun Bude Wuta A Jami'ar Mombasa Da Ke Kasar Kenya
Oct 10, 2017 12:00Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ta sanar da cewa: Wasu gungun mahara sun kai harin wuce gona da iri kan jami'ar Mombasa da kudancin kasar Kenya, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu na daban.
-
Taron Wakilan Kasashen Afrika Da Faransa Don Bunkasa Dangantakar Bangarorin Biyu
Oct 07, 2017 06:44An kammala taron kwanaki biyu na kasashen Afrika da Faransa don bunkasa dangantaka tsakanin bangarorin biyu a fagen tattalin arziki, siyasa da kuma zamantakewa.
-
Kenya: An Yi Taho Mu Gama A Tsakanin 'Yan Sanda Da "Yan Hamayyar Siyasa
Oct 06, 2017 18:08Masu Zanga-zangar dai suna yin kira ne da a kori jami'an hukumar zaben kasar da aka zarga da magudi.
-
AU Ta Yi Kira Kan Warware Rikicin Kenya Cikin Ruwan Sanyi
Oct 05, 2017 09:48Kungiyar tarayyar Afrika ta AU, ta yi kira da a warware rikicin Kenya cikin ruwan sanyi, gabanin sabon zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa ranar 26 ga wannan watan.
-
Kenya: An Rufe Jami'ar Nairobi Saboda Zanga-zangar Dalibai Masu Adawa Da Gwamnati.
Oct 04, 2017 07:55A jiya talata ne dai shugaban jami'ar ta Nairobi Peter Mbithi ya sanar da rufe jami'ar saboda Zanga-zangar dalibai masu adawa da gwamnati.
-
'Yan Sandan Kenya Sun Tarwatsa 'Yan Adawa Masu Zanga-Zanga A Birnin Nairobi
Oct 02, 2017 11:23'Yan sandan kasar Kenya sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa 'yan adawa masu gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar, Nairobi, wadanda suka fito don bukatar da a sallami jami'an hukumar zaben kasar da suka gudanar da zaben shugaban kasar da aka soke.
-
Kotun Kolin Kenya Ta Bukaci A Binciki Hukumar Zabe
Sep 24, 2017 17:05Kotun kolin a Kanya ta bukaci da a binciki hukumar zaben kasar akan kura kuran da aka samu a babban zaben kasar da aka gudanar a watan Agustan da ya gabata.
-
Shugaban Kasar Kenya Ya Zargi Kotu Da Yin Juyin Mulki
Sep 21, 2017 20:01Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata ya soki matakin kotun Kolin kasar da yin juyn mulki, inda ya ce hukuncin da ya haramta nasarar zabensa a matsayin sabon shugaban kasa ya yi sabani da ra'ayin al'ummar kasar kenya.
-
Kotun Kolin Kenya Ta Soki Hukumar Zaben Kasar Saboda Batun Sakamakon Zabe
Sep 21, 2017 05:44Kotun kolin kasar Kenya ta soki hukumar zaben kasar saboda gazawar da ta nuna wajen tantance sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan da ya kama kafin ta fitar da shi.