AU Ta Yi Kira Kan Warware Rikicin Kenya Cikin Ruwan Sanyi
(last modified Thu, 05 Oct 2017 09:48:31 GMT )
Oct 05, 2017 09:48 UTC
  • AU Ta Yi Kira Kan Warware Rikicin Kenya Cikin Ruwan Sanyi

Kungiyar tarayyar Afrika ta AU, ta yi kira da a warware rikicin Kenya cikin ruwan sanyi, gabanin sabon zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa ranar 26 ga wannan watan.

AU ta ce ta na ci gaba da bibiyar yadda batun siyasar kasar na baya bayan nan ke tafiya, biyo bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na soke zaben ranar 8 ga watan Augustan da ya gabata.

Sanarwar da AU ta fitar a jiya Laraba, ta ce Shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su kauracewa yin duk wani abu ko furuci da zai iya haifar da koma baya ga tsarin demokradiyyar kasar, ko zubar da nagartar zaben da aka shirya gudanarwa nan gaba.